Masha Allah har yanzu ana karrama wacca taciyo gasar al’qur’ani ta duniya baki daya gwaman gwambe ya karrama ta da kyautar kudi kimanin naira…
Gwamnan Gombe Inuwa yahaya ya baiwa hafiza Hajara Dan Azumi da manya manyan kyaututtuka da gwazon da tayi na lashe gasar musabaƙa ta duniya da ankayi a kasar Jordan.
Gwamnatin Jihar Gombe a Nijeriya ta karrama matashiyar nan Hajara Ibrahim Ɗan’azumi, wadda ta lashe musabaƙar Alƙur’ani ta duniya ta mata da aka gudanar a ƙasar Jordan.
A yayin karramawan a ranar Alhamis, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar ya miƙa mata kyautar naira miliyan biyar da kujerar Hajji da kuma sanar da ita ɗaukar nauyin karatunta da gwamnati za ta yi.
Kazalika an bai wa makarantar Islamiyyar da Hajara ke zuwa kyautar naira miliyan biyar.
“Na yabawa malamai da kuma dalibai gwaraza da sunka je sunka ciyo mana kyaututtuka da dauko matsayi wanda na tabbata idan jihar gombe mu ka tsaya a kowa ne fadi zamu iya zamowa zakuru, saboda muna da mutane haziƙai wanda kuma in sha Allahu suna mana abinda ya kamata”-inji inuwa yahaya.