World News

Ana tsaka da sallar Jumu’ah acikin raka’a ta biyu kawai yan bindiga suka bude wuta har sun hallaka mutum 2 a jahar kaduna…

Wannan wace irin masifa ce? Ana tsaka da sallar Jumu’ah cikim raka’a ta biyu yan bindiga suka bude wa masallatan wuta har sun kashe mutum biyu nan take tare da raunata wasu a jihar Kaduna

A yau Jumu’ah da wajen misalin ƙarfe biyu na rana ana tsaka da sallar Jumu’ah a Angwar Makera, dake Kwasakwasa cikin karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna, yan bindiga suka bude wuta kan masu sallar inda a nan take mutum biyu suka rasu, wasu da dama suka sami munanan raunuka.

Kamar yadda majiyar Katsina Daily News ta rawaito, a lokacin da yan bindigar suka iso masallacin ana cikin raka’a ta biyu, da zuwansu suka ci gaba da harbin kan mai uwa da wabi, dalilin da ya jawo wasu da dama suka arce ba su tsaya aka kammala sallar da su ba.

Tuni dai aka yi wa mutum biyun da suka rasu zana’ida a tsohuwar makabartar Kuyallo kamar yadda addini ya tanada

Majiyar tamu ta Daily Post ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Mansir Hassan , game da neman karin bayani a kan hari, sai ya ce yana cikin mintin da ya shafi tsaro a cikin lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button