World News

Da Duminsa: Sojin Najeriya tayi Nasarar Aika Wani na Hannun Damar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Moɗi  Zuwa Barzahu bayan sunyi bata kashi…

Yanzu nan majiyarmu ta samu labari mai daɗi wanda majiyarmu ta samu ta hannun Muhammad Aminu kabir kan nasarar da rundunar sojojin Nijeriya sunka samu na kashe wani na hannun damar ƙasurgumi ɓarawon da ya addabi yankin.

A ƙoƙarin ta na kakkaɓe ƴan ta’addar daji daga dazukan jihar Katsina, rundunar sojin Najeriya tayi dirar mikiya a dazukan Kurfi da Safana inda tayi nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindiga na hannun damar moɗi moɗi mai suna, Maikusa.

Jami’an dai sun kashe Maikusa da wasu ɓarayin Ukku ne a ranar Litinin 4 March 2024, yayinda suke musayar wuta tsakanin su da ɓarayin a ƙananan hukumomin Kurfi da Safana jihar Katsina kazalika kuma rundunar tayi nasarar ƙone maboyar ƴan bindigar dake waɗannan dazukan.

Yayin fafatawar ƴan ta’addar sun ɗauki tsawon lokaci suna ɓarin wuta da Jami’an tsaro amma dai Jami’an tsaron sun ci galaba akan su inda suka gudu a hargitse yayin da wasu suka bakunci lahira.

Bayan da ƙura ta lafa Jami’an sunyi nasarar samun Bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, ƙwarkwaron Alburushi guda Ukku da kuma Alburusai Guda 65 masu lambar 7.62 mm sai bindigar gargajiya da kakin Sojoji Guda.

Rundunar ta lalata maboyar ɓarayin a garuruwan Wurma, Shaiskawa, Yauni, da Dogon Marke duk a cikin ƙaramar hukumar Kurfi, haka nan kuma rundunar ta lalata maboyar ɓarayin dake Ummadau da Zakka cikin ƙaramar hukumar Safana.

Tushan labarin: hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button