Tofah: za’a shawo kan matsalar Man fetur A Nijeriya nan da shekara 10 – NNPC menene ra’ayinku akan hakan jama’a…
A wani alkawari na magance matsalar karancin man fetur, kamfanin na NNPC ya tabbatar da cewa za a shawo kan dukkan matsalolin da ke da alaka da Hakan nan da Shekaru 10 masu zuwa.
A yayin da ake fara taron kasa da kasa kan makamashi na Najeriya karo na bakwai a Abuja A jiya Talata, Mele Kyari, babban jami’in gudanarwa na kamfanin NNPC, ya bayyana wa mahalarta taron.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye ya fitar, ya bayyana kudurin yin aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar karancin makamashi da samar da wadata ga al’ummar Najeriya.
“Ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki a kan kudirin kamfanin na yin aiki tare da su domin dakile gibin makamashi da samar da wadata ga ‘yan Nijeriya, ya kara da cewa daga dukkan alamu za a kawo karshen matsalolin karancin makamashi a kasar nan da shekaru 10 masu zuwa,” inji sanarwar.
Tushan labarin: Hausaloaded.com