Uncategorized

An k@she mace mai juna biyu da wasu mutane shida, a yayin da ake kokarin karbar shinkafar keasatam mai rahusa karan ta karin bayani…

Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da ke gwajon shinkafar da karfin tuwo.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba.

Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani bangare na yunkurinta rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da ake fama da ita fadin kasar.

Jaridar Aminya na ruwaito cewa ,Wata ganau mai suna Comfort James ta ce jami’an kwastam “sun yi bakin kokarinsu wajen shawo kan lamarin amma abin ya gagara, kuma ba a tsara abin sosai ba.

“Dun da cewa ’yan sanda sun zo amma ba su wani taimaka ba, shinkafarsu su ma suka zo karba.”

Amma a martaninsa game da lamarin, kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce, “ba zan iya cewa an samu asarar rai ba, amma akwai wadanda suka sume kuma an kai su asibiti.

“An fara abin cikin lumana a gaban shugaban hukumar kwastam na kasa, har zuwa misalin karfe 5 na yamma.

“Jami’anmu sun kula da jama’a sosai, har zuwa lokacin da aka samu turureniyar daga baya.”

Amma wani likita, Adunola Yemoka, ya wallafa a shafinsa na X cewa daya daga cikin mutanen da aka kai asibiti ya rasu daga bisani.

Hakazalika jami’yyar APC reshen Jihar Legas ta sanar cewa wata daga cikin mambobinsu mai suna Misis Adebanjo Comfort Funmilayo na daga cikin wadanda suka rasu a sakamakon turureniyar sayen shinkafar.

– Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button