Uncategorized
Wata kiristan ta suma sau biyu kafin karfe 4 na rana yayin gwada yin azumin Ramadan da tayi, an garyaza da ita asibiti…
Wata kirista Eniola Fagbemi wacce ke auren wani musulmi a Kudu ta yi kurarin cewa azumin musulmi bashi da wuya tunda suna yin sahur kuma su sha ruwa lokacin magriba, don haka tace za ta jaraba don ta tabbatar masa,
Majiyarmu ta ruwaito cewa Sai dai bayan Eniola ta yi sahur wajajen 4:30 na asuba tun wajen karfe 12 na rana ta fara fita hayyacinta, kan kace kwabo ta suma sau Biyu wajajen ƙarfe 4 na yamma ba arziki aka kwashe ta sai asibiti.
Tace masu yin azumi jarumai ne maganar gaskiya, mutum ya daina cin abinci tun 4:30am har zuwa 6:30pm baci ba sha ae sai jarumai
Allah ya taimaka an ceto rayuwar ta a asibitin Saanu Hospital dake garin Mokola.