Yadda na tsere daga hannun yan bindiga bayan ɗaya daga cikinsu ya maida ni matarsa har na haihu Inji wata matashiya da ta kubuta karan ta karin bayanin…
Yadda na tsere daga hannun yan bindiga bayan ɗaya daga cikinsu ya maida ni matarsa har na haihu Inji wata matashiya da ta kubuta karan ta karin bayanin…
“Mun yi kwanaki tara muna tafiya cikin daji, lokacin da ƴanbindiga suka kama mu,” a cewar wata matashiya da ta kuɓuto daga hannun ɓarayin daji.
Matashiyar da BBC ta sakaya sunanta ta ce ƴanbindiga sun yi garkuwa da su ne lokacin da suke kan hanyar zuwa biki a yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Ta shaida wa BBC yadda rayuwa ta kasance da ita a hannun ɓarayin dajin.
Ta ce ta shafe kusan shekaru uku a hannun yanbindigar, har ta kai ga wani daga cikinsu ya aure ta, kuma ta haifa masa ɗa.
Ta ce lokacin da aka shiga daji da sau ɗaya kawai aka tsaya kafin su isa inda za a tsare su kusan kwata tara suna tafiya. “Rayuwa ce mai wahala” .
“Idan ka nuna ba ka son inda suka kai ka a nan ne za ka sha wuya, domin tamkar bawa za su mayar da kai duk wasu aikace-aikace kai za ka yi tun daga shara, da wanke-wanke har da girki,” in ji ta.
Wani abin tashin hankali ga wannan matashiya dai, shi ne auren da aka daura mata tare da ɗaya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su.
BBC ta ganta ɗauke da jariri ɗan watanni biyu, wanda ta ce mahaifinsa ɗanfashin daji ne, kuma sai da ya kira mahaifinta a waya ya shaida masa zai aure ta har ma da faɗin sadaki.
”Ina zaune a gidansa na gama dinkawa matar shi hijabi ya shigo, ya tambayi wace ce ni aka ce baƙuwa ce. Daga nan sai ya tambaye ni ko zan yi aure ko zama haka zan yi?
“Na shaida masa ni ba zan yi aure ba ban kuma ce ina so ba. Daga nan ya kira mahaifina ya sanar da shi zai aure ni ga kuma sadakina nan.”
“Wannan jaririn da ke hannuna warannin shi biyu, kuma na shafe shekara biyu da wata 10 a hannun barayin kafin Allah ya ba ni sa’a ni da wata makwabciyata muka tsere.”Matashiyar ta ce a kan idonsu aka kawo fasinjojin jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, da aka yi garkuwa da su a watan Maris 2022.
“An zuba su ne a wani dogon ɗaki mai langa-langa. Ta kuma ce cikin wadanda suka kawo sun har da kasurgumin ɗanfashi Dogo Gide da ya addabi wasu yankunan Najeriya.
”An kulle su a cikin ɗakin, ba a barinsu fita akwai kuma masu gadinsu.
“Cikin shugabannin akwai Dogo Gide na taɓa ganin shi – dogo ne fari amma ba sosai ba, bai cika zama a wurin ba saboda suna yawan samun saɓani a tsakanin su ‘yan bindigar,” in ji ta.
Dogo Gide na daga cikin manyan ɓarayin daji da suka addabi sassan Zamfara da Neja da Kaduna har zuwa Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa shi ya yi garkuwa da ɗaliban makarantar Yauri a jihar Kebbi.Matashiyar ta ce sun shirya tserewa tare da wata mata da suka shaƙu.
Ta ce misalin 12 na dare, ta goya jakar kayanta da kuma ɗanta, suka yi ta keta daji.
Ta ce sun shafe kwanaki uku suna tafiya kafin suka isa wani gari.
”Daman wani ya taba nuna mana hanyar ya ce za ta kai mu gari, ai kuwa muka yii ta tafiya har kwanaki uku kafin Allah ya kawo mu cikin garin Mina na jihar Neja.”
Duk da wannan matashiya ta samu kuɓuta, tare da samun ‘yanci da guzurin jariri, ta ce har yanzu akwai sauran ‘yan uwanta da ke tsare a hannun barayin da suka sace su a birnin Gwarin jihar Kaduna, tana kuma fata da kira ga sojojin Najeriya su kubutar da su.
Allah ne kawai ya san adadin mutanen da masu garkuwa da mutane domin kudin fansa suka sace a Najeriya, inda wasu kan samu ‘yanci bayan ‘yan’uwa da abokan arziki sun biya kudin fansa.
Satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, musamman a jihohin arewacin kasar.
Barayin daji kan far wa garuruwa da kauyuka tare da sace mutane maza da mata, hatta yara da tsofaffi ba su tsira ba.
A wasu lokutan, sukan shiga har gidajen jama’a tare da sace iyalai ko duk wanda tsautsayi ya fada kan shi, kuma batun guda daya ne sai an biya makudan kudade kafin a sako su.
Yawancin manyan titunan arewacin Najeriya dai sun zama shiga da alwalarka, sakamakon yadda wadannan ‘yanfashin ke tare hanyoyin da sace fasinjoji tun daga kan na motocin haya har zuwa na gida.
Kuma har yanzu akwai wadanda aka yi garkuwa da su da babu amo babu labari, kuma ‘yan’uwansu ba su da masaniya kan halin da suke ciki, ko a mace ko a raye, kamar yadda BBC Hausa ta tattara rahoton