World News

Wani matashi da ake zaton dan jihar Katsina ne ya rasu a Lagos karan ta karin bayani akan sa, tushan labari “katsina daily news”.

Assalamu Alaikum Katsina Daily News Sunana Nazir Muhammad, muna tare da wani bawan Allah a Lagos da ya bayyana mana sunansa da Muhammed, tsawon lokaci ba mu taba ganin ya je gida ba, ya kwashe kusan shekara biyar ko sama da haka a can, ba wanda ya taba ba labarin garin da yake, sai dai mun taba ganin ID card dinsa ya nuna kamar daga Katsina yake wajen yankin Daura.

Bayan ya kamu da rashin lafiya jiya ya rasu a jiya Jumu’ah, don haka muke so a sanar ko yan uwansa don sun sami wannan labarin su san halin da dan uwansu yake ciki.

Domin karin bayani ga lambar Sarkin Hausawan Sharif Maina na yankin da yake zaune a Lakwai karamar hukumar Ibeji Leki 08027324959 sarkin hausawa sheriff maina

Allah Ya gafarta masa Ya sa yan uwansa su ga wannan sanarwar don sanin halin da dan uwamsu yake ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button