World News

Masha Allahu; Haddar Al’Kur’ani: Daliban da su ka yi sauka za su juya – Mallam Aminu,👇👇👇

Masha Allahu; Haddar Al’Kur’ani: Daliban da su ka yi sauka za su juya – Mallam Aminu

Shugaban makarantar Sidratul Muntaha Littahafizul Qur’an Waddirasatul Islamiyya, Mallam Aminu Khamis Abubakar ya ce, matuƙar gwamnati da masu hannu da shuni za su rinƙa tallafawa makarantun Islamiyya da abubuwan da ya sawwaƙa, babu makawa za a samu cigaban da ya dace.

Mallam Aminu Khamis ya bayyana hakan ne a yayin saukar karatun Al-ƙur’ani mai girma, da makarantar ta gudanar na ɗalibai 31 karo na 4, a cikin unguwar Sabuwar Gandu da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.
“Ɗaliban mu da su kayi saukar karatun Al-ƙur’anin za su juya daga farko, domin karatun ya zauna musu yadda ya kamata” Inji Mallam Aminu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, al’umma da dama ne su ka samu damar halartar bikin saukar, daga ciki kuwa akwai Mallam Yahya Sheikh Zakari mai ƴan mari da dai sauran manyan baƙi daga sassa daban daban na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button