World News

Da Duminsa: Rundunar yan sandan jihar Katsina ta sanya tukuicin naira miliyan hamsin N50m ga duk wanda ya bada labarin yadda za a kama wasu yan bindiga biyu…

Da Duminsa: Rundunar yan sandan jihar Katsina ta sanya tukuicin naira miliyan hamsin N50m ga duk wanda ya bada labarin yadda za a kama wasu yan bindiga biyu da suka addabi jihar

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta sanya kyautar naira miliyan hamsin, ga duk wanda ya taimaka wa yan sandan da wani labari na inda za a gano wasu manyan yan bindiga biyu da suka addabi jihar Katsina don kamo su.

Kamar yadda Katsina Daily News ta ga sanarwar da kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu da har jaridar Daily Trust ta wallafa, ya bayyana sunayen yan bindigar da Modi Modi da kuma Jan Kare, da suka fitini yankin Kankara da Safana dake nan cikin jihar Katsina

Rundunar ta kara da cewa duk wanda ya sami labarin inda yan bindigar suke, da ya garzaya kai tsaye zuwa shalkwatar yan sandan dake Katsina don kai masu ruhuto, ko a kira su ta wadannan lambobin 07015142112 08023871144,”

Tushan labarin; Katsina daily news

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button