World News

Maroko ta soma jefa wa jama’ar Gaza kayan agaji ta jirgin sama karan ta yadda komai yafaru…

Yakin da Isra’ila ke yi a kan Falasɗinawa da ke Gaza – wanda ke cikin kwanaki na 158 – ya kashe aƙalla mutane 31,112, galibi yara da mata, tare da jikkata 72,760.

Ƙasar Maroko ta shiga sahun wasu ƙasashen duniya domin kai kayan agaji Gaza inda a karon farko ita ma ta jefa wa jama’ar Gaza kayayyakin agaji ta jirgin sama.

Jaridar Hespress ta ruwaito wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila tana cewa gwamnatin Rabat ta buƙaci aika jiragen agaji zuwa Tel Aviv da arewacin Gaza.

Gwamnatin ta Morocco tare da haɗin gwiwar Isra’ila sun tura jirage shida ɗauke da kayan agaji.

Wani labari : Jirgin ruwa ɗauke da tan 200 na abinci na hanyar zuwa Gaza

Jirgin ruwa ɗauke da kusan tan 200 na abinci ya kama hanyar zuwa Gaza daga wata tashar ruwa ta Kudancin Cyprus, a wani yunƙuri na buɗe wata sabuwar hanya ta ruwa domin kai agaji ga jama’ar Gaza.

Jirgin ruwan na ƙungiyar agaji da ceto ta Open Arms an hange shi yana barin tashar ruwa ta Larnaca ɗauke da kusan tan 200 na shinkafa da fulawa da abincin gina jiki.

Wannan aikin kai agajin, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ke ɗaukar nauyinsa, inda ƙungiyar World Central Kitchen ke shiryawa sai kuma ƙungiyar agaji ta Proactiva Open Arms da ke ƙasar Sifaniya ke bayar da jirgin dakon kayan.

~TRT AFRIKA HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button