Madallah A koda yaushe na Allah basa ƙarewa kullum sai kyakkyawar tarbiyyar da nuna tawali’u na musulmai fitowa yake a fili abun da yafaru dame P.O.S
Madallah A koda yaushe na Allah basa ƙarewa kullum sai kyakkyawar tarbiyyar da nuna tawali’u na musulmai fitowa yake a fili abun da yafaru dame P.O.S
Lamarin ya faru ne a watan Disamba na shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.
Wani mai sana’ar POS a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa yayin da yake son tura masa naira dubu 10, kamar yadda rundanar ƴan sanda reshen jihar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a watan Disamba na shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.
TRT AFRIKA HAUSA ya ruwaito cewa,Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ƴan sandan ya fitar ta ce sun kwashe kimanin wata uku suna bincike kafin su gano mutumin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.
Rundunar ƴan sandan ta ce tuni mai POS ɗin ya mayar wa ɗan kasuwar kuɗinsa wato naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in (9,990,000:00). Jin daɗin haka ya sa ɗan kasuwar ya ba mai POS ɗin kyautar naira 500,000. Kazalika rundunar ƴan sandan ta yaba da kyakkyawan halin mai POS ɗin kuma ta buƙaci sauran jama’a da su yi koyi da shi.
A kwanakin baya ma an samu wani ɗan agaji mai suna Salisu Abdulhadi wanda ya tsinci naira miliyan 100 a jihar Katsina kuma ya yi cigiyarsu har sai da aka gano ainihin mai kuɗin, inda aka mayar masa da kuɗinsa.
TRT AFRIKA HAUSA