World News

Kaduna: Ɗaliban mu 287 ƴan bindiga su ka sace a kuriga — inji Wani Malami ga dai yadda abun yafaru dalla dalla…

Wani malamin makarantar firamare da sakandare su kusan da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna ya baiyana cewa ɗalibai 287 ƴan bindiga su ka kwashe a makarantar.

A jiya Alhamis ne ƴan bindigar su ka kutsa kai cikin makarantar, wacce take haɗe da firamare da sakandare, suka yi awongaba da ɗaliban

Malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi, wanda ya kubuta a harin ya baiyana cewa ɗalibai 287 ne aka sace a makarantar.

Sani Abdullahi ya ce “A bangaren sakandare ɗalibai 187 ne suka bace amma bangaren firamare ɗalibai 125 da farko ba a gansu ba amma daga bisani guda 25 sun dawo.”

Malamin wanda ya bayyana hakan lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ziyarci makarantar domin gani da ido yadda lamarin yake , ya kara da cewa “na shigo makaranta misalin karfe 7:45 sai na shiga ofishin principal kuma sai ya ce min in waiga baya, ina juyawa sai naga ‘yan bindiga sun kewaye makarantar”.

“Mun ruɗe bamu san inda zamu ba, kafin da suka tafi damu daji sai muka canza hanya,” in ji Sani Abdullahi.

Malamin makarantar ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutum daya.

Yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.

Ya bayyana cewa ana cikin wani hali na fargaba tun bayan sace daliban a safiyar Alhamis.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce “Babu wani gida a Kuriga wanda wannan abin bai shafe shi ba”.


~BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button