World News

Ina ake so talaka yasa kansa Buhun masara mai cin tiya 40 ya kai Naira 73,000 a katsina ga farashin sauran jahohin arewa…

Ina ake so talaka yasa kansa Buhun masara mai cin tiya 40 ya kai Naira 73,000 a katsina ga farashin sauran jahohin arewa…

A makon nan dai, al’ummar kudancin Nijeriya  sun dara, sakamakon  saukar farashin kayan abinci, yayin da a yankin Arewacin kasar kuwa, farashin wasu daga cikin kayan abincin ya fi na makon da ya gabata. A kasuwar Mile 12 International Market Lagos dai, a makon jiya, farashin buhun Masara mai cin tiya 40, ya kai N60,000, sai dai, a wannan makon an samu ragin kudi har N5,000, inda farashin buhun masarar ya kama N55,000.

A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuwa, farashin buhun masarar bai sauya zane ba, an dai sayi masarar kan kudi N57,000 a wancan satin, hakan aka saya a wannan makon ma. Sai dai, a kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuma,  masara ta fi sauki a wancan makon, sama da makon da muke ciki, inda aka sayar da buhun  N57,000 a makon da ya gabata, yayin da wannan makon kuwa kuɗin buhun masarar ya shilla zuwa N73,000.

A makonni biyu da suka gabata dai, an sayi masara kan kudi N62-65,000 a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, amma a wannan makon kuɗin buhun masarar  ya kama N55,000 -N57,000.

Ita kuwa kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, masarar ta fi sauki a makonnin da suka gabata sama da yanzu, inda a wadancan makonnin aka sayar da buhun masara N42,000, amma kudin buhun a makon nan, ya kai N55,000 cif. Haka kudin buhun masarar ya ke a kasuwar Dandume na jihar Katsina,kudin ya kama N55,00

A kasuwar Giwa ta jihar Kaduna ma Masarar ta haure, inda a makonnin da suka shude aka sayar da ita N51,000, amma a makon nan kuɗin buhun masara N55,500 ne.

Shinkafar gida ta fi  sauki a makonnin da suka gabata a kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda a wancan makon kuɗin ya kama N120,000, yayin da a makon nan aka sayi shinkafar N125,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna.

A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuwa, kuɗin buhun shinkafar gida ya kama N108,000, a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma an samu karin N5,000, kan kudin buhun shinkafar na baya, inda aka sayar da buhun N115,000. Sai dai a makon nan, kudin buhun N120,000 ne, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuma kuɗin shinkafar Hausa N60,000 cif cif.

Ita ma dai shansharar shinkafar ta fi sauki  a baya sama da na wannan makon, a Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, inda makon da ya gabata kudin buhun shinkafar mai bawo ya kama N40,000-43,000. Sai dai a makon nan kuɗin N58,000 ne -59,000.

Buhun shinkafar Hausar  N130,000-135,000 ne a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.

Idan muka leka bangaren shinkafar waje, ta fi sauki a makonnin da shuka shude sama da na yanzu da ake ganin kamar ta yi sauki.inda makon nan  kuɗin ya kama N75,000 a kasuwar Mile 12 International Market Legos,da wancan makon aka saya N70,000 daidai.

A kasuwar Kashere da ke jihar Gombe kudin Shinkafar N85,000 ne hakan batun ya ke a kasuwar a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano,amma an samu saukin N3000 a kasuwar Zamani dake jihar Adamawa,inda kuɗin Shinkafar N82,000.

Zamu ƙarƙare farashin kayayyakin abincin na  makon da farashin Taliyar Spaghetti ,a Dukkanin kasuwannin dai farashi yafi na makon biyu da suka shuɗe Tsada,inda aka sayar da  kwalin  Taliyar N14,500 a kasuwar Mile 12 International Market  Legos,Amma an samu sassaucin N1000 a  kasuwar Dawanau  dake jihar Kano,inda kuɗin kwalin Taliyar ya zama   N13,500 ,,haka nan batun bai sauya zani a kasuwar Kashere dake jihar Gombe.

A Mai’adua jihar Katsina kuwa kudin a wannan makon ya kama  N13,000 cif.

A kasuwar Zamani dake jihar Adamawa kuwa,N13,800 ne kudin ko wani kwali guda na Spaghettin.

Tushan labari: dclhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button