World News

Gwanin Sha’awa Wata Baturiya Mai Shekaru 62 da Haihuwa tayi Saukar Alkur’ani a Jahar Kano…👇👇👇

Gwanin Sha’awa Wata Baturiya Mai Shekaru 62 da Haihuwa tayi Saukar Alkur’ani a Jahar Kano..

Aure ne ya kawo Matar, mai shekaru 62 da haihuwa zuwa garin Kano shekaru 30, inda ta Auri wani dan kasuwa Marigayi Alhaji Ibrahim Sambo.

Da take zantawa da manema labarai, tace ta musulunta ne shakaru goma da suka gabata, inda daga nan ta fara koyon karatun Alkur’ani.

A cewar ta, ta fara koya ne a gida, duba da shekarunta, a karkashin wata Malama mai suna Malama Hafsat

“Na ji dadi da na karbi Addinin Musulunci. Ina samun farin ciki da kwanciyar hankali. Sannan saukar Alqur’ani din nan ma ta bani farin ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button