World News

Daga Mai alfarma sarkin Musulmi A fara duban jinjirin watan Ramadan daga yau Lahadi…

Majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya NSCIA a Ƙarƙashin Jagorancin shugabanta kuma mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta Buƙaci al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar nan dasu nemi Jinjirin watan Ramadan na Shekarar 2024 (1445AH) Daga yau Lahadi

Majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya NSCIA a Ƙarƙashin Jagorancin shugabanta kuma mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta Buƙaci al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar nan dasu nemi Jinjirin watan Ramadan na Shekarar 2024 (1445AH) Daga Gobe Lahadi.

Farfesa Salisu Shehu, Mataimakin Sakatare Janar na NSCIA ne ya bayyana hakan a Jiya Juma’a.

A cewarsa, Sarkin Musulmi Abubakar yana taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar azumin watan Ramadan na Shekarar ta 1445 Bayan hijira.

Sarkin Musulmi ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su nemi jinjirin watan Ramadan na shekarar 1445 bayan faduwar rana a ranar Lahadi 10 ga Maris, 2024, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban. shekara ta 1445 AH.

“Idan aka Samu Ganin jinjirin watan da maraice, to mai martaba (Sultan) zai bayyana Litinin 11 ga Maris 2024, a matsayin ranar farko ga watan Ramadan 1445. Idan kuma ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, to ranar Talata 12 ga Maris, 2024, ta zama ranar daya ga watan Ramadan, 1445H,”

Ya ci gaba da cewa, a halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki, majalisar ta yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su kara kai agaji ga marasa galihu a cikin unguwanninsu kafin watan Ramadan, da kuma bayan watan Ramadan.

Majalisar ta kuma shawarci ‘yan kasuwa da kada su rika tara kayan abinci, ko kuma su kara farashin kayayyakin masarufi a lokacin azumi.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan watan na Ramadan su yi addu’ar Allah ya baiwa Falasdinawa goyon bayansa, ya kuma ‘yantar da su daga azzalumai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button