Uncategorized

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano ya bada umarnin kama tsohon Sarkin Kano Aminu Bayero…

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a kama tsigaggen Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cikin gaggawa saboda yunƙurin haifar da tashin hankali a jihar.

A daren jiya ne dai a asirce aka shigo da tsohon Sarkin cikin birnin Kano a yunkurinsa na komawa fadar ta karfi da yaji bayan kwana biyu da Gwamna ya sauke shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, an tabbatar da cewa sabon sarki Muhammadu Sanusi ll ya shiga fadar a hukumance tare da gwamna, mataimakin gwamna, kakakin majalisar dokokin jihar da sauran manyan jami’an gwamnati da misalin karfe 1:00 na daren juya Juma’a.

“A matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar, mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kama tsohon sarkin nan ba tare da bata lokaci ba saboda tada hankalin al’umma da yunkurin lalata zaman lafiyar da jihar ke amfana” in ji sanarwar.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar ya rattaba hannu kan dokar majalisar masarautun jihar Kano (gyara mai lamba 2) ta shekarar 2024.

Dokar da aka yi wa kwaskwarima ta soke kafa masarautun Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya a jihar.

Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button