World News

Abun Ban tausayi da takaici: Yadda yan bindiga suka kori mutanen garin Wurma da wasu garuruwa a Katsina kalli abun da yafaru…

Ƴanbindiga masu satar mutane sun tilasta wa al’ummar wasu garuruwa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya yin gudun hijira.

Yanbindigar sun abka ne garin Wurma da ke ƙaramar hukumar Kurfi inda suka bude wuta, lamarin da ya tilasta wa mutanen yankin gudun hijira domin tsira da ransu zuwa makwabta.

“Babu kowa a garin duka an fito,” kamar yadda wani mazauni garin Wurma ya shaida wa BBC

Gwamnatin jihar Katsina da ta tabbatar da al’amarin ta ce matsalar ta kuma shafi garuruwan Lambo da Guda da ke yankin na Kurfi.

Kwamishinan tsaron jihar Katsina Dakta Nasir Baangida Ma’azu ya ce ƴanbindigar sun matsawa yankin.

“Shiga ta farko sun bi gida-gida, shiga ta biyu kuma suka ƙone sansanin ƴansanda, dalilin da ya sa mutane suka gudo,” a cewar Kwamishinan.

A ranar Juma’a wasu al’ummar yankunann na karamar hukumar Kurfi sun gudanar da zanga-zanga kan kan ƙamarin matsalar tsaron da ke addabarsu.

Sun ce an kashe mutane da sace da dama sakamakon yawaitar hare-haren na ƴanbindiga baya ga asarar dimbin dukiya.

“Da magariba suka kawo mana hari, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sun kashe akalla mutane biyar, dukkansu magidanta.”

Sun kwashi dukiya mai yawa wannan abin ya bai wa mutane haushi, don haka duka aka fito daga garin Wurma aka yi bore saboda mutanenmu na ganin ita ce hanyar da za ta tilasta wa gwamnati ɗaukar mataki,” in ji wani mazauni yankin.

Ya kuma ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a garin Birchi da ke cikin karamar hukumar Kufin, da su ma ke fama da matsalar ta ɓarayin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa.

Tushan labari: katsina daily news

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button