Abin alfahari: Yadda wani dan agaji ɗan nan jihar Katsina ya tsinci naira miliyan ɗari N100m ya kuma yi cigiyar mai su ya mayar masa karan ta karin bayanin yadda akai…
Abin alfahari: Yadda wani dan agaji ɗan nan jihar Katsina ya tsinci naira miliyan ɗari N100m ya kuma yi cigiyar mai su ya mayar masa karan ta karin bayanin yadda akai…
Ya kau sha Kyaututtuka da lambobin yabo
Ƙungiyar Izala ta ƙasa, JIBWIS ta karrama wani matashin ɗan agaji da ya tsinci kuɗi sama da naira miliyan 100, sannan ya mayar da su.
Cikin wani sako da ƙungiyar reshen jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce matashin ɗan agajin mai suna Salihu AbdulHadi Kankia, ya taka rawar gani, wanda ya kai a jinjina masa.
A wurin rufe taron ƙara wa juna sani na malamai masu gabatar da tafsiri, Daraktan Agaji na ƙasa Injiniya Mustapha Imam Sitti ya gabatar da matashin wanda ya tsinci jaka cike da makudan kuɗi da suka kai sama da naira miliyan 100 a Kankia da ke jihar Katsina.
”Salihu ya ɓoye kuɗin a gida, sannan ya garzaya zuwa ofishin ƴansanda ya sanar musu cewa ya tsinci jaka a yi cigiya wa al’umma amma jakar tana wurinsa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Kan wannan abin a yaba ne ƙungiyar ta Izala ta karrama matashin da lambar yabo tare da ba shi kyautar kujerar Hajjin bana.
”Sannan kuma Hon. Abdulmalik Zannan Bangudu (Ɗan Agaji kuma Dan Majalisa a Jihar Zamfara) ya bashi kyautar miliyan biyu”, kamar yadda sanarwar ta bayyana
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed ya ba shi kyautar mota kirar bas don ya kama sana’a..
Tsintar makudan kuɗi a kuma mayar da su musamman a wannan yanayi da ake ciki na matsin rayuwa, abin a yaba ne.
Ko a shekarar da ta gabata ma wani matashi mai tuka keke Napep a Kano ya tsinci kuɗi kimanin naira miliyan 14 tare da mayar da su ga mai su.
Lamarin da ya sa matashin ya samu kyaututtuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen jihar.
Haka ma a shekarar da ta gabata, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya karrama wata mata da ta tsinci wasu makudan kuɗaɗe sannan ta mayar da su a lokacin aikin hajjin da ya gabata