Masha Allah: An cafke yan banga kusan goma da ake zarginsu da k@she babban limamin garin Mada ta jihar Zamfara karanta karin bayani domin sanin suwaye…
An kama wasu da ake zargin sune suka kashe malamin addinin musulunci a Zamfara, kuma za a gurfanar da su gaban kuliya, kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.
An kama akalla mutum goma da ake zargin Ƴankungiyar Ƴanbanga ne kan kisan gillar da aka yi wa wani Malamin a jihar Zamfara.
Wasu gungun Ƴanbanga sun kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a ranar Talata a garin Mada da ke karamar hukumar Gusau.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa wadanda ake zargin da hukumomi suka kama Ƴanbanga ne ba jami’an hukumar kare jama’a ta jihar (CPG) ba.
A cewar sanarwar, Ƴanbanga da aka kama, gwamnatin jihar ba ta ba su izinin gudanar da duk wani nau’in aikin tsaro ba, saboda ba sa cikin jami’an tsaron al’umma CPG.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta samu labarin kisan da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada ba bisa ka’ida ba.
“Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke Ƴanbangan da ake zargi da aikata wannan danyen aikin.kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki wannan lamari da muhimmanci kuma ta himmatu wajen ganin an gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan kisan gilla a gaban kotu. Za a yi duk mai yuwuwa don ganin an yi adalci a tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Kungiyar Tsaron Al’umma wacce gwamnati ta kirkiro na aikin tsare al’umma ne ba cin zarafin su ba, saboda haka za mu tabbatar irin haka bai auku ba a faɗin jihar.
“Muna so mu fayyace cewa Ƴanbanga da ake zargi da aikata kisan gilla ba su da wata alaka da jami’an tsaron al’ummar jihar Zamfara.
“Jami’an kare hakkin jama’a, rundunar tsaro ta al’umma, an kafa su ne domin kare al’umma ba wai kuma su gallaza musu ba a jihar.
Tushan labarin: Katsina daily news.