World News

Ƙarancin abinci: CBN ya bada tallafin taki buhu miliyan 2.15 domin rabawa manoma a Nijeriya, Shin menene ra’ayinku akan hakan…


Ma’aikatar noma da wadatuwar abinci ta karbi buhunan takin zamani guda miliyan 2.15 daga babban bankin Najeriya, CBN

Ma’aikatar noma da wadatuwar abinci ta karbi buhunan takin zamani guda miliyan 2.15 daga babban bankin Najeriya, CBN.

Za a raba takin ne ga manoma domin dakile hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar tare da bunkasa samar da abinci da kuma wadatar sa.

Abubakar Kyari, ministan noma da wadatuwar abinci wanda ya yi jawabi a wajen taro a yau Laraba a Abuja, ya nuna godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da CBN bisa wannan karimcin.

Kyari ya tabbatar wa Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, cewa za a yi amfani da kayan cikin adalci tare da kai wa manoman da ke da buƙata.

Tun da fari Cordoso ya bayyana farin cikin da zaiyarar da kuma miƙa takin ga ma’aikatar noma, wanda a cewar sa zai yi maganin hauhawar farashin abinci.

A cewarsa, farashin kayan abinci na daga cikin muhimman abubuwan da ke tattare da hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce babban bankin na CBN na da burin inganta hadin gwiwarsa da ma’aikatar domin inganta samar da abinci.


Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button