YANZU YANZU : An buɗe bodar Nijeriya da Nijar wanna fata za kuyiwa juna…
YANZU YANZU : An buɗe bodar Nijeriya da Nijar wanna fata za kuyiwa juna…
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duka sauran takunkuman da Nijeriyar ta saka wa Nijar.
YANZU YANZU : An buɗe bodar Nijeriya da Nijar
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni a buɗe iyakokin ƙasar da na Nijar nan take.
TRTAFRIKA ta ruwaito cewa,Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duka sauran takunkuman da Nijeriyar ta saka wa Nijar.
Shugaban ya bayar da umarni kan a ɗage waɗannan takunkuman da aka saka wa Nijar nan take: –
1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakannin Nijeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.
2- Dakatar da duka cinikayya tsakanin Nijeriya da Nijar, da dakatar da duka ayyukan da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.
3- Rike kadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.
4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.
5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu
Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire
takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea.
TRTAFRIKA Hausa