Tofah; fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi ƙarar Gwamnatin Kano a gaban Babbar Kotun jihar akan wannan dalilin karanta karin bayani…
Wannan dai na cikin ƙunshin takardar ƙarar da Murja ta shigar bisa wakilcin lauyoyinta — A. U Hajji da S.S Shehu — mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Fabarairun 2024.
A ƙunshin ƙarar da Akawun Kotun, Adam S. Adam ya rattaba hatimi da kuma sa hannu, Murja ta buƙaci a shiga tsakaninta da Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kwana Huɗu.
Aminiya ta ruwaito cewa, cikin jerin waɗanda ƙarar da Murja ta shigar ta shafa akwai Antoni-Janar na Jihar Kano da Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, da Hukumar Hisbah da Hukumar Asibitocin Kano da Babban Asibitin Masu Larurar Kwakwalwa da ke Dawanau.
Takardar ta nuna cewa, Babbar Kotun ta cimma muradu huɗu daga cikin jerin buƙatu bakwai da lauyoyin Murja suka gabatar wa Mai Shari’a Nasiru Saminu.
Sai dai Aminiya ta lura cewa, daga cikin buƙatun lauyoyin Murja da kotun ta yi watsi da su, har da ta neman mayar wa wadda suke wakilta wayarta ta hannu kirar iPhone da kuma katin banki na ATM.
Da wannan hukuncin ne kotun ta kuma ɗage ƙarar zuwa 20 ga watan Maris na 2024.
Fitacciyar jarumar nan ta dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi ƙarar Gwamnatin Kano a gaban Babbar Kotun jihar.
Wallafawa ranar: 01/03/2024 – 17:59
Minti 1
Tushan labarin; hausaloaded.com