Talaka ina zai saka kansaJama’ar garin ƴargoje sun tare babban titi suna zanga-zanga rashin tsaro a jihar Katsina ku kuran ta ne yafaru yau…
Ɗaruruwan mutane ne da sanyin safiyar yau Talata suka fito kan Titi a Ƴargoje dake cikin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina inda suke nuna rashin jin daɗin su yadda ƴan ta’addar daji suka maida yankin nasu kufai.
Wannan tare hanya domin nuna rashin tsaro da ake fama da rashin tsaro domin nuna fushin su ba sabon abu bane, wannan gangamin ɗaruruwan mutane sun nuna fushin da halin ko oho da shuwagabanni ke yi ana Wasa da rayuwar al’umma inda wani marubuci Muhammad Aminu kabir ne ruwaito wa majiyarmu Wannan labari.
Ɗaruruwan mutane ne da sanyin safiyar yau Talata suka fito kan Titi a Ƴargoje dake cikin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina inda suke nuna rashin jin daɗin su yadda ƴan ta’addar daji suka maida yankin nasu kufai.
Al’ummomin ƙauyuka sama da Arba’in ne yanzu haka suke gudun hijira a yankunan Ƴargoje da Burdugau a ƙaramar hukumar ta Kankara jihar Katsina.
Kimanin mutane 5,000 ne ke gudun hijira a yankin sakamakon hare haren da ƴan Bindiga ke kai masu ba ƙaƙautawa a waɗannan yankunan.
Ko a daren jiya Litinin dai ɓarayin sun kai farmaki tare da kashe kimanin Mutane Huɗu, yayinda suka saka wasu Mutanen cikin gidajen su tare da banka masu wuta inda suka ƙone ƙurmus.
Wani Mazaunin yankin ya shaida mana cewa Al’umma suna cikin tsananin tashin hankali yanzu haka a garin Ƴargoje duk an rufe Makarantun garin an baiwa ƴan gudun hijira wuraren banda waɗanda suke cikin gidajen Mutane kowane Ɗaki zaka iya tarar da Mutane sama da Ashirin suna zaman hakuri.
Kodai satin da ya gabata sai da Gwamnatin Jihar Katsina Ta aike da tawaga ta musamman zuwa Ƴargoje domin jajanta ma Mutanen dake gudun hijira a yankin.
Tushan labari: hausaloaded.com.