Labari mai dadin ji: Muna gab da bude bodar Nijeriya zuwa Nijar umurni kawai muke jira – Inji hukumar kwastam karan ta karin bayanin aciki wani hanzari ba…
Hukamar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya, Kwastam, ta ce tana jiran ta samu umarni daga gwamnatin Najeriya, kafin ta buɗe iyakar ƙasar da makwabciyarta Nijar.
Wannan shi ne karo na farko a hukumance da hukumar ta fito ta bayyana haka, duk da kiraye-kirayen da jama’a ke ta yi kan a bude kan iyakar.
Hukumar ta ce nan ba da wani lokaci mai tsawo ba ne ta ke sa ran za a buɗe bakin iyakar.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma, ECOWAS ko CEDEO ta bayyana ɗage takunkuman da ta ɗorawa Nijar, lamarin da ya kai ga rufe bakin iyakokin ƙasashen ƙungiyar da Nijar na tsawon watanni.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan yulin 2023 ne Najeriya ta rufe iyakokinta da Nijar lamarin da ya haifar da ƙaruwar matsin rayuwa ga ƴan Najeriyar da kuma Nijar ɗin.
A halin yanzu akwai ɗaruruwan motocin dakon kaya ɗauke da kayan abinci da na masarufi da aka hanawa shiga Najeriyar.
Ƴankasuwar Najeriyar sun yi maraba da umarnin cire takunkumin da ECOWAS ta yi, sai dai kawo yanzu ba su samu shigo da kayan ba saboda ci-gaba da kasancewar bakin iyakar a rufe.