Innalillahi 😭 Wata Budurwa ta Mutu a sakamakon cin garin Kwaki da tayi wanda ake zargin ya kulle mata ciki lokacin da take matsananciyar Jin Yunwa👇👇
Wata Budurwa Fiddausi Mahmud dake garin Rimin Hamza a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ta Mutu a sakamakon cin garin Kwaki da tayi wanda ake zargin ya kulle mata ciki lokacin da take matsananciyar Jin Yunwa
Mahaifin Fiddausi Malam Mahmud Abdullahi ya shaidawa Rahma TV cewa iyalansa sun wuni Basu samu Abincin da zasuci ba abinda yasa ya fita nema , Kuma ya kawo musu Garin Kwaki .
Wakilinmu Tukur S Tukur ya raiwaito mana cewa Duka yayan Magidancin su 6 harda uwar gidansa Saida cikinsu ya kulle wasu sukayita Amai da gudawa saidai matsalar Marigayiya Fiddausi yafi makamari .
Magidancin Malam Mahmud Abdullahi Yana Gadin Baburan Adaidaita Sahu ne a un seeguwarsu inda yake samun kasa da Naira 500 a Rana , Wanda yace ko kudin Garin Kwaki Rabin Kwano Basu kaiba .
Tuni akayi Janaizar Marigayiya Fiddausi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar